A ranar asabar da ta gabata ne kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Zamfara ta gudanar da zabe a matakin jihar baki daya, inda ‘yan takara suka fafata da juna tun daga matakin shugaban jiha har sauran mukamai 21 da aka fafata akansu.
Kamar yadda sabon shugaban kungiyar ya aiko wa Aminiya ta e-mel, an yi zaben cikin tsanaki da kwanciyar hankali tare da bin dokokin da Kwamitin Zaben ya gindaya, ciki har dokar da ta hana wadanda ba sa da ci kakken rijista da mallakar ID Card din kungiyar shiga zaben.
Zaben ya zama zakaran gwajin dafin ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da takwarorinsu na wasu jihohi da su tashi tsaye na tabbatar da dimukradiyya ba ra’ayoyin wasu kalilan ba.
Bayan kammala zaben, Kwamared Hafizu Balarabe Gusau ne.
‘Rashin gaskiya ne yake durkusar da kamfanonin fatu’
Daga Jabiru A. Hassan, a Kano
An bayyana cewa rashin gaskiya da rikon amana su ne suka sanya kamfanonin fatu suke durkushewa ba tare da cimma bukatar da aka fasu ba.
Wannan tsokacin ya fito ne daga wani mai sana’ar fata wato Alhaji Yakubu Maifata Tsanyawa a zantawarsu da wakilinmu, inda ya ce sana’ar fatu da kiraga harka ce mai amfani da albarka, sai dai rashin tsayar da gaskiya ya sa mafiya yawan kamfanonin da ake da su na hada-hadar sayen fatu da kiraga suke “mutuwa tun kafin aje ko’ina.”
Ya ce: “Wajibi ne a rika gudanar da wannan sana’a bisa amana da gaskiya ta yadda kowa zai fuskanci alherin da ke cikin sana’ar hada-hadar fatu da kiraga a wannan kasa tamu, tare da jaddada cewa idan aka tsaftace sana’ar ko shakka babu masu yin ta za su ci moriyar harkar musamman ganin cewa sana’a ce mai bunkasa tattalin arzikin kasa.”
Dangane da batun yadda kamfanonin sayen fatu da kiraga suke gudanar da al’amuransu kuwa, Alhaji Yakubu ya bayyana cewa a halin yanzu ana samun ci gaba a fannin sayen fata saboda kamfanonin hada-hadar fatu da kiraga da ke Jihar Kano suna kokarin ganin samun kyakkyawar fahimta tsakanin su da masu kai masu kaya a kodayaushe.