✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi yunkurin kashe ni saboda waka – kayawa

Aminiya ta samu tattanawa da mawaki Aliyu Dahiru wanda ake yi wa lakabi da Aliyos kayawa inda ya bayyana dalilan da suka sanya ya tsunduma…

Aminiya ta samu tattanawa da mawaki Aliyu Dahiru wanda ake yi wa lakabi da Aliyos kayawa inda ya bayyana dalilan da suka sanya ya tsunduma harkar waka da kalubalen da ya fuskanta.

Za mu so ka gabatar da kanka?

An haife ni a garin Kayawa da ke cikin Karamar Hukumar Dutsi da ke cikin Jihar Katsina a shekarar 1995 kimanin shekaru 22 da suka gabata. Na yi makarantar firamare a kayawa wacce ake kira kayawa Model da na gama sai na shiga sakandire ta kayawa daga nan ban ci gaba ba saboda wasu dalilai amma ina sa ran zan ci gaba da karatu har na cimma burina.

Me ya kawo ka Jihar Kano har ka fara waka?

Harkar waka ce ta kawo ni Kano. Dalili shi ne wakokinmu na Nanaye sun fi karbuwa a Jihar Kano. Na fara waka ne tun shekarar 2010 kimanin shekaru kusan bakwai ke nan. Kamar yadda na gaya maka na fi ba da karfi a wakokin Nanaye amma ina yin wasu wakokin na daban kamar na soyayya da na siyasa da wakar bege da ta’aziya da aure da suna da makamantansu.

Wakoki nawa ka rera?

A kalla na rera wakokin kimanin 85 a dakin daukar sauti wato studiyo. Akwai wakar da na yi ta “So Sinadarin Aure” da wakar “Soyayya mai sa zumunci” da wakar “So gamon Jini ne” da wakar “ Haduwa daya na kamu da son ki masoyiya” sai wakar da na ta aure ta tarihi mai lakabin “Jamila da Jamilu” da wakar da na yi wa ubangidana ta “Dallatu”. Ita ma na samu daukaka sosai.

Wace waka ka fi so cikin wakokinka kuma me ye dalilinka?

Wakar da na fi so ita ce wakar “Aure”. Dalilai biyu ne suka sa na fi son wakar. Na farko ita ce wakata ta farko da na raira a sutudiyo ba tare da na gamu da wata matsala ba. Na yi ta cikin nishadi da nutsuwa. Na biyu kuma wadanda na yi wa wakar sun yi murna da farin cikin kuma wakar ta samu karbuwa a wurin mutane. Akwai mutane da yawa da suka nuna min so kwarai da gaske. Akwai mata da yawa da suka ce suna so na tsakani da Allah. Akwai wacce ta ce za ta dauki nauyina na cigaba da karatu kuma za ta aure ni.

Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu?

Na samu nasara ta samun dimbin masoya ciki da wajen Najeriya. Na samu kudi  da rufin asiri. Sai dai godiyar Allah. Na yi abokan arziki da yawa kuma waka ta hada ni da jama’a iri-iri.

Wadanne kalubale ka fuskanta?

Na fuskanci kalubale masu yawa.daya daga cikin kalubalen da ba zan manta ba shi ne wani lokaci da na je zan yi waka aka hana ni, aka yi mini wulakanci. Akwai yarinyar da na nema aka hana ni aurenta aka rika cewa wai mawaki za ta aura, dan iska saboda haka aka raba mu karfi da yaji..

Shin da aka hana ka auren yarinyar saboda sana’arka ta waka ya ka ji?

Gaskiya na ji bakin ciki na shiga cikin kunci. Irin yadda al’umma suke yi mana kallon ’yan iska marasa tarbiya wani babban kalubale ne da ke damun mawaka. Ina so na yi amfani da wannan da na fadakar da jama’a cewa mu ba ’yan iska ba ne. Muna da tarbiya, muna yin ibada kamar kowa da ambaton Allah kamar yadda kowa yake yi. Wannan zargi ne wanda bashi da tushe bare makama. Mawaka suna taimakawa al’umma domin waka, hanye ce mafi sauki ta isar da sako ga al’umma.

Ka taba fuskantar kalubalen shiga kurkuku ko makamancin haka?

Akwai lokacin da na yi wata wakar siyasa da na yi aka rika yi min barazanar za a kashe ni ko azuba min guba a abinci. Har aminina aka tuntuba don a zuba mini guba a abinci amma Allah da ikonsa sai ya ce shi ba zai yarda a hada kai da shi ba a cuce ni. Na ji tsoro kwarai da gaske amma da na samu kwarin gwiwa daga wurin aminaina sai na tsaya kyam na ci gaba da harkar wakokina ba cuta ba cutarwa ba tare da wani tsoro ba.