Jami’an tsaro sun cafke wani mutum da ya yi yunkurin kashe Limamin Masallacin Harami a yayin da yake cikin gabatar da hudubar Sallar Juma’a.
Mutumin ya fito daga cikin sahu a guje ya nufi mumbarin da Sheikh Bandar Baleela ke gabatar da huduba a ranar 21 ga Mayu, 2021.
- Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya rasu
- Ta auri maza bakwai don samun haihuwa da kowanensu
- An sace attajiri da matar dan siyasa a Kaduna
“Mutumin na dauke da makami a lokacin da ya nufi wurin da limamin ke gabatar da huduba,” inji shafin Masallacin Harami, bayan ya fitar da bidiyon yadda lamarin ya faru.
A bidiyon an ga wani mutum sanye da Harami yana tawo a guje, yana kaiwa kusa da mimbarin limamin, sai askarawa suka tare shi suka cukwikuye shi, nan take aka yi awon gaba da shi.
Gwamnatin kasar Saudiyya ta ba da muhimmanci ga tsaron Masallatan Harami da Limamansu, kasancewar ba karon farko ba ke nan da ake kai musu hare-hare.
Hare-haren da aka kai wa Limaman Masallacin Harami
Kimanin shekara 20 da suka gabata, wani mutum ya yi yunkurin daba wa Sheikh Abdulrahman Sudais wuka a lokacin da yake zaman Tahiyar karshe a lokacin da yake limanci a Masallacin Harami.
A 2011 kuma wani mutum ya ture daga daga cikin limaman Masallacin Harami, wato Sheikh Abdullahi Jahani, ya dauki makirfon ya yi ta ihu.
Kafin shi wani mutum ya taba neman kai wa Sheikh Ali al-Hudhaifi hari a yayin da malamin yake limancin Sallar Subahi.
Harin ’yan bindiga Masallacin Harami
Shekara 1979, ’yan bindiga kusan su 200, karkashin jagorancin Juhayman al-Utaybi, sun kai kazamin hari a Masallacin Harami a lokacin aikin Hajji, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
A lokacin, bayan liman ya idar da sallah, sai Juhayaman da almajiransa suka tunkude shi suka kwace makirfon, suka fara jawabi da cewa Mahadi ya dawo.
Gabanin haka, sun riga sun shigo da makamansu a cikin makara; sai da ta kai ga an nemi dauki tare da shafa musu gas mai guba kafin a murkushe su.
An dauki kwanaki ana gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati, da mutanen da suka kai harin a lokacin aikin Hajji.
A karshe dai gwamnatin Saudiyya ta yanke wa Juhayaman da almajiran nasa hukuncin kisa.
Tun daga wannan lokaci kasar Saudiyya ke bayar da tsaro na musamman a Masallacin Harami da limamansa.