A shekaranjiya Lraaba ne aka gudanar da wasan kwallon kafa a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta don karrama tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo.
Wasan, ya kunshi ’yan kwallo biyar-biyar ne daga kowane bangare da suka hada da bangaren shugaba Obasanjo da kuma na Gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun.
Dubban jama’a ne suka halarci filin wasan don kashe kwarkwatar idanu.
Obasanjo wanda ya jagoranci ’yan kwallon da suka hada da Farfesa Akin Mabogubje da kuma Dokta Femi Olopade da sauran mutum uku daga bangarensa su suka samu nasara da ci 2-1 a wasan.
Cif Olusegun Obasanjo ya nuna cewa da sauransa a harkar wasan kwallo bayan ya jefa kwallayen biyun da suka ba bangarensa nasara a wasan.
A daya bangaren kuwa, Gwamnan Ogun Ibikenle Amosun da wadansu mutum hudu ne suka fafata a wasan da bangaren su Obasanjo.
An shirya wasan ne don taya Obasanjo murnar cika shekara 78 kuma an gudanar da wasan ne a tsawon minti 60.