A ranar Lahadi ne wasu Gwamnonin Najeriya suka yi dafafi a Fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wajen nema wa dan Shugaba Muhammadu Buhari aure.
An yi wa Yusuf Buhari baiko da diyar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, inda tawagar gwamnonin bisa jagoranci Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ta wakilci iyalan Shugaba Buhari a matsayin masu nema.
- ‘Na yi wa matar aure fyade a kullum na tsawon watanni biyar’
- NDLEA ta kama hodar iblis mai nauyin kilo 394 a Taraba
Tawagar wakilan ta nema wa Yusuf auren Zahra Nasir Ado Bayero a hannun Sarkin Kano, kasancewarsa waliyyinta kuma yaya ga Sarkin Bichi.
Aminiya ta samu rahoton cewa, za a gudanar da shagalin bikin auren a tsakanin watan Agusta zuwa Satumbar bana.
Tawara da ta ta yi wad an shugaban kasar wakilci ta hada da Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari.
Sauran ’yan tawagar sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sherrif, tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun da kuma Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.
Bayanai sun ce daga bisani tawagar ta garzaya garin Bichi inda ta gaishe da Sarki kuma mahaifin wacce ake neman auren a wurinsu.