A ranar Talatar da ta gabata ce hedkwatar ’yan sandan Jihar Gombe ta yi wa jami’anta 93 karin girma zuwa matakai daban-daban.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Bello Makwashi da taimakon Mataimakinsa suka lika wa jami’an sababbin mukamansu.
Da yake jawabi lokacin da lika mukaman, Kwamishinan ya hore su cewa su dauki sababbin mukamin nasu a matsayin wata dama ta ci gaba da bauta wa kasarsu wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu.
Bello Makwashi ya sake yin roko a gare su da su kare martabar aikin dan sanda a duk inda suka samu kansu a bisa amincewa da yardar da ake da su gare su.
Ya hori sauran ’yan sanda cewa su sadaukar da kai wajen aiki tukuru da kuma kasancewarsu masu hakuri sannan su jira nasu lokacin.
’Yan sanda 93 din da aka kara wa girman sun hada da Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda wanda ya zama Na’ibin Kwamishina, sai Mataimakan Sufurtandan ’Yan sanda (DSP) su takwas da aka kara wa girma zuwa Sufurtandan (SP) sai Mataimakin Sufurtandan (ASP I) takwas da suka zama DSP, da kuma sufetoci 76 da suka zama ASP II.
Ita ma Jami’ar Hulda da Jama’a ta ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Mary Obed Malum ta samu karin girma zuwa Sufurtanda, inda shi ma mai taimaka mata a ofishin PPRO, Sufeto Yusuf Balami, ya zama ASP II.
Da take godiya a madadin sauran, SP Obed Mary Malum, godiya ta yi, sannan ta tabbatar da cewa za a same su masu da’a a aikinsu.