Yayin da ake ci gaba da yi wa al’ummar kasar Afirka ta Kudu allurar rigakafin cutar COVID-19, Shugaban Kasar, Cyril Ramaphosa ya bi sahun wadanda aka fara yi wa allurar a asibitin Khayelitsha dake birnin Cape Town.
Jim kadan da yi masa rigakafin ranar Laraba, shugaban ya nuna matukar farin cikinsa da yadda daga karshe aka kaddamar da shirin a kasar.
- Ko sisi ba za mu biya diyya kan daliban Kagara ba —Gwamnatin Neja
- Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke gabansa a Kano
Ya ce, “Yin rigakafin akwai sauri matuka, akwai sauki kuma babu zafi ko kadan. Ina kira ga dukkan jami’an lafiya da suma su bi sahu a yi musu.
“Muna farn cikin farata a tsakiyar watan Fabrairu kamar yadda muka yi alkawari a baya, duk kuwa da cewa rigakafin AstraZeneca da muka sayo ba ta nuna wani tasiri sosai ba wajen yaki da cutar, sabanin 501Y.V2 wacce a yanzu ita ce ta fi yawa a kasarmu,” inji shugaban.
Shugaba Ramaphosa ya ce nan ba da jimawa ba dukkan masu rike da madafun iko a kasar su ma za su fito a yi musu a bainar jama’a a kokarin da suke yi na karfafa gwiwar mutanen kasar.
Ya ce yana fatan ganin cewa ta hanyar tasirin rigakafin za a samu nasarar dakile kaifin cutar a kasar.
Shi ma Ministan Lafiyar kasar, Zweli Mkhize an yi masa rigakafin ne tare da Shugaban Kasar da wasu manyan jami’an Ma’aikatar lafiyar kasar.
Akalla kwayoyin rigakafin 80,000 ne daga kamfanin Johnson & Johnson aka shiga da su kasar ya zuwa ranar Talata kuma za a yi amfani da su ne a kan jami’an lafiyar kasar.