Rahotanni daga Saudiyya sun bayyana cewa an yi wa Sarki Salman bin Abdulaziz gwajin lafiyarsa a Asibitin
Cikin sanarwar da Masarautar Saudiyya ta fitar ta ce: “Shugaban masu yi wa Masallatai Biyu Masu Tsarki hidima, Sarki Salman bin Abdulaziz (Allah ya ci gaba da kare shi) ya bar asibitin kwararru na Sarki Faisal a Riyadh bayan da likitoci suka yi nasarar binciken lafiyarsa da safiyar yau, godiya ta tabbata ga Allah.”
- Firaministocin EU 3 sun ziyarci Kyiv yayin da hare-haren Rasha ke kara tsananta
- Hare-haren masu jihadi sun addabi gwamnatin soji a Burkina Faso
Haka kuma shafin sada zumunta na Haramain Sharifain, ya wallafa hotuna da bidiyon Sarkin Salman yayin da yake fitowa daga asibitin bayan likitoci sun sallamo shi.
A cikin hotuna da bidiyon sarkin mai shekara 86 da aka wallafa, an ga dansa Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman cikin masu take masa baya.
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Yulin 2020 an kwantar da Sarki Salman a asibiti na tsawon kwana 10 saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa.