Gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta sanar da yi wa fursunoni sama da 800 afuwa, a yayin da ta gudanar da faretin nuna kwanji a babban birnin kasar don bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai shekaru 75 da suka wuce.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa a ranar Asabar ce shugaban gwamnatin soji Min Aung Hlaing ya ba da wannan umarni na sakin fursunoni 814, abin da aka saba yi a rana irin wannan.
- An yi haduwar ba zata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a Sakkwato
- Dan Sarauniya ya kai wa Shekarau ziyara
Kasar ta fada cikin rikici tun a shekarar da ta gabata bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya haddasa zanga zanga da ta yi sanadin mutuwar sama da farar hula 1,500.
Ana bikin an shekara shekara ne don tunawa da ranar da jagoran gwagwarmayar neman yancin kai, Aung San da kabilu da dama suka shiga yarjejeniyar yanto Burma daga mulkin mallakar Birtaniya.
A bara ce Janar Min Aung Hlaing ya sanar da cewa za a yi wa fursunoni 5000 saboda dalilai na jin kai biyo bayan dubban mutanen da aka kama saboda zangar-zangar adawa da juyin mulkin da aka yi a watan Fabrairun shekarar da ta gabata.