✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Musulmai feshin barkonon tsohuwa a filin Idi a Habasha

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron kasar sun ce sun sun tsare mutum 76 bisa zargin tayar da tarzomar.

Ana fargabar cewa jami’an tsaro a Addis Ababa, babban birnin Habasha, sun fesa barkokon-tsohuwa kan wasu Musulmai da suka taru domin gudanar da sallar Idi.

Dubban Musulmai ne suka taru ranar Litinin a babban filin wasan birnin inda kuma a nan ake sallar Idi amma rikici ya barke ko da yake babu rahoton rasa rai.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan da aka tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Musulmai da Kiristoci a sassan kasar bayan an kashe Musulmai 20 da ke halartar jana’iza a makon jiya a Arewacin Habasha.

Bayan aukuwar lamarin a birnin Gondar, an gudanar da jerin zanga-zanga a wurare da dama da kuma tarzoma ciki har da kona akalla coci uku a kudancin kasar.

Matakin da jami’an tsaro suka dauka na fesa barkonon-tsohuwa kan Musulman zai iya dagula lamura kamar yadda BBC ya ruwaito.

An ga hotunan mutane suna tserewa yayin da ake wurga musu barkonon-tsohuwa da kuma mata da ke neman ‘ya’yansu cikin kaduwa.

Rundunar ‘yan sandan Addis Ababa ta dora alhakin lamarin kan “wasu tsirarun mutane” kuma ta ce an lalata wurare da dama.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron kasar sun ce sun sun tsare mutum 76 bisa zargin tayar da tarzomar.