Wasu da ba a san ko su wane ba sun yi wa wasu kananan yara biyu yankan rago a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Mietti Allah (MACBAN) na karamar hukumar, Ya’u Idris, ya bayyana wa wakilinmu cewa an yi wa yaran yankan rago ne a wata gona a safiyar Lahadi.
- Adamawa: Sanarwar ‘nasarar Binani’ daidai ne —Kwamishinan Zabe
- Wutar Lantarki: Katse layin KEDCO a Kano somin-tabi ne —TCN
Ya’u ya ce yaran da aka kashe ’yan shekaru bakwai da kuma 12 ne, kuma zai sanar da DPO da kuma Kwamandan Rundunar Soji a Operation Safe Haven na Bassa kafin a dauke gawarwarkin.
A cewarsa, daukacin yankin Bassa na zaune lafiya, don haka babu wanda zai iya cewa ga abin da yaran suka yi da har wani za iya yi musu wannan kisan gilla.
Don haka ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su kamo wadanda suka yi wa yaran yankan rago domin su fuskanci hukunci.
Ya ce sun dauki abin da ya faru a matsayin kaddara, amma ya bayyana cewa duk da haka, hukunta masu laifin zai zama darasi ga duk masu tunanin yin hakan a nan gaba.
Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sandan jihar ta Filao DSP Alabo Alfred, ya kuma tura masa rubuaccen sako domin neman karin bayani, amma bai amsa ba tukuna.