Gwamnatin kasar Norway da tallafin Majalisar Dinkin Duniya da hadin gidauniyar Festula Foundation da kuma Gwamnatin Jihar Gombe sun yi wa mata 61 aikin ciwon yoyon fitsari a Gombe.
Mataimakin Darakta mai kula da ayyuka a Ma’aikatar lafiya ta jihar, wanda kuma shi ne likitan da ya yi musu aiki Dokta Muhammad Buwa Garba, ya jinjina wa hukumomin da suka dauki nauyin aikin tare da yin kira ga sauran kungiyoyin da ba na gwamnati da su yi koyi da su.
Dokta Garba ya ce ba duka matan da aka yi wa aiki ne ’yan Jihar Gombe, ba akwai wadanda suka zo daga jihohin Zamfara har ma daga babban birnin tarayyar Abuja.
Ya ce kaso 60.7 cikin 100 na matan ne ’yan Gombe, ragowar kason ’yan wasu jihohi ne.
Ya kara da cewa wannan matsalar ta fi yawan faruwa da mata ne a lokacin da ba su samu halarta asibiti don yin awon ciki a lokacin da suka samu juna biyu ba, ko kuma wadanda suka je amma ba su samu kulawar da ta dace daga likitoci ba.
Sannan sai ya ce a karon farko jihar Gombe ta samu cibiyar aikin ciwon yoyon fitsari a Asibitin Kwararru na Jihar, inda ya ce a baya idan za a yi aikin ciwon sai dai idan likitoci sun kawo ziyarar tallafi.
Shi ma jami’in gidauniyar, Musa Isa, wanda ya samu wakilcin Abubakar Ibrahim, ya ce gidauniyar tasu ta zabi ta taimaka wa mata masu fama da wannan larurar ce saboda mafi yawansu masu karamin karfi ne da al’umma ke kyamar su a lokacin da suka samu wannan ciwo.
Abubakar Ibrahim, ya ce a lokacin da mace ta samu juna-biyu wasu ba su cika samun damar zuwa asibiti dan awon ciki ba saboda suna karkara ko saboda yanayin halin rayuwa da hakan kan haifar musu da wannan matsalar.
Wasu mata da Aminiya ta zanta da su da aka yi wa aikin sun bayyana jin dadinsu ga masu da tallafin.
A cewarsu, tsawon wadannan shekaru ba sa iya shiga jama’a saboda ana tsangwamarsu bisa larurar da suke fama da ita.