✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa mata 1000 aikin ciwon yoyon fitsari a Bauchi

A cikin shekara biyar da suka gabata, an yi wa mata fiye da 1000 aikin ciwon yoyon fitsari (BBF) a Asibitin Cutar Yoyon fitsari na…

A cikin shekara biyar da suka gabata, an yi wa mata fiye da 1000 aikin ciwon yoyon fitsari (BBF) a Asibitin Cutar Yoyon fitsari na Kasa da ke Ningi a Jihar Bauchi.

Babban Likitan Asibitin Dokta Nasiru Umar Ibrahim ne ya sanar da haka lokacin da yake jawabi a karshen taron ba da horo kan aikin yoyon fitsari na wata guda da aka yi wa likitoci da ma’aikatan jinya a Bauchi, wanda Asusun Kidayar Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) da hadin gwiwar Gwamnatin Kanada da Gwamnatin Tarayya suka dauki nauyin gudanarwa a asibitin da ke Ningi.

Dokta Nasitu ya ce a kowace shekara ana yi wa mata sama da 200 aiki tun lokacin da aka kafa asibitin kimanin shekara biyar da suka wuce, kuma majinyata da ke dauke da cutar yoyon fitsarin daga jihohi da dama da wasu kasashen da ke makwabta ne suke zuwa jinyar yoyon fitsari a asibitin.

Babbar Jami’ar da ke kula da cutar yoyon fitsari a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Misis Ogunmayiwa Peters, ta ce mata dubu 150 ne suke fama da cutar yoyon fitsari a kowace shekara. Sai ta yi kira a kara samar da wadataccen kudi da za a yi maganin cutar saboda yawan karuwa da take yi kowace shekara.

Sai ta ce akwai wani shiri mai karfi da gwamnati ke yi na kara bude cibiyoyin kula da cutar yoyon fitsari a sassan kasar nan domin marasa lafiya su samu wurare masu sauki kuma kusa da su da za su rika zuwa jinya.

Ta ce tuni aka mika wa gwamnati bukatar kara samar da kudi don kula da cutar kuma akwai alamar cewa za a iya samun karin kudin.

Babban Jami’in ba da horon Dokta Musa Elisha ya ce mahalarta taron na wata guda sun fito ne daga jihohin Bauchi da Sakkwato kuma a lokacin da suke ba da horon an yi wa mata 50 da ke dauke da cutar aiki, kuma UNFPA tare da hadin gwiwar Kanada da Gwamnatin Tarayya ne suka dauki nauyin yi musu aikin.

Likitan ya ce bayan mata dubu 150 da ke kamuwa da cutar kowace shekara ana kuma samun karin sama da dubu 20 da ke karuwa kowace shekara wanda akwai matukar bukatar a rage yawan aukuwar lamarin.