Sarkin Askar Fataskum da ke Jihar Yobe, Dokta Aminu Abdullahi, ya yi wa marayu da ’ya’yan marasa galihu 100 kaciya kyauta a Jihar.
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin har da masu larurar gani 20 da kurame guda biyar.
- AFCON2021: Dalilai 3 da suka sa aka yi waje da Najeriya
- Gwamnatin Kano ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke Jihar
Sarkin Askar, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Wanzamai na shiyar Arewa maso Gabas, ya gudanar da aikin ne da tallafin Sarkin Fika, Alhaji Dokta Muhammad Ibn Abali Idrissa.
Dokta Aminu Abdullahi, ya ce wannan shi ne karo na biyu da fara wannan kaciyar, inda ko a 2020 ya yi wa marayu sama da 200, a kyauta.
Ya ce a lokacin da yake zuwa yi wa yara kaciya ne a garin Fataskum, wasu iyaye suka koka masa cewa akwai yara marayu da ba su da wanda zai biya musu kudin yin kaciyar, wanda ya ga cancantar yi musu kaciyar kyauta.
A cewarsa yin hakan tamkar sadakatul jariya ne, inda ya ce duk yaron da aka yi wa kaciyar zai iya sa wandonsa nan take.
A nasa jawabin, Sarkin Askar Sarkin Kano, kuma Shugaban Sarakunan Aska na Najeriya, Dokta Muhammad Yunusa Nabango, kiran wanzaman ya yi da cewa su kara jajircewa wajen ganin sun inganta sana’arsu sannan kuma suyi koyi da irin abin da Sarkin Askar Fataskum din yake yi.