✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa manyan jami’an ’yan sanda 19 karin girma a Gombe

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Oqua Etim, ya lika wa wasu manyan jami’an rundunar a Jihar su 19 sabbin shaidar karin girma. Daga cikin mutum 19 da…

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Oqua Etim, ya lika wa wasu manyan jami’an rundunar a Jihar su 19 sabbin shaidar karin girma.

Daga cikin mutum 19 da suka samu karin girman har da mutum daya mai mukamin DCP da ACP guda daya da CSP 7 da kuma DSP 10.

Da yake taya su murna bayan lika musu sababbin mukaman nasu, Kwamishina Oqua Etim, ya taya su murna inda ya hore su da su kara jajircewa a aiki domin hazakarsu da kwazo ne suka kai su ga karin girman.

Ya kuma yi kira ga wadanda ba su samu karin girman a yanzu ba da su jira nasu yana zuwa a nan gaba.

Kwamishinan ya kuma ja hankalinsu da su kara kulawa da dawainiyar iyalansu da kyau ta hanyar kyautata musu saboda su shaida cewa sun samu canji, sannan da kula da karatun ’ya’yan su wanda hakan ne zai sa albashin ya kara albarka.

Ya kuma ja kunnensu da su guji cin zarafin farar hula domin su hadiman al’umma ne kuma duk halin da ake ciki su yi aiki yadda doka ta tanada.

Ya ce duk wanda aka samu da cin zarafin al’umma doka za ta yi aiki a kansa.

Da yake jawabin godiya a madadin manyan jami’an da suka samu karin girman, CSP Jonah Adukwa, ya gode wa Babban Sufeton ’Yan sanda na kasa da kuma hukumar kula da ayyukan yan sanda tare da kwamishinan yan sandan jihar Gombe bisa yi musu wannan karin girma.

CSP Jonah, ya kuma yi alkawarin cewa za su kara kwazo a aikin domin sai anyi aiki tukuru ake samun karin girma kara, sannan kuma a cewar sa za su kiyaye doka da kaucewa cin zarafin al’umma.