Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wani malami da ya yi wa dalibansa 13 fyade har suka dauki ciki a wata makarantar kwana ta addini a kasar Indonesiya.
Kotun ta yanke wa malamin suna Herry Wirawan, mai shekara 36 hukuncin ne bayan ta kama shi da laifin yi wa dalibai masu kananan shekaru fyade, inda takwas daga cikinsu suka dauki juna biyu.
- Ba wanda ya isa ya tilasta min karbar rigakafin Coronavirus —Djokovic
- An tona asirin manyan ’yan sanda da NDLEA bayan Abba Kyari ya kwana a tsare
Kotun da ke zamanta a yankin Bandung da ke Yammacin Java ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, a yayin da gwamnatin Indonesiya ta ce Shugaba Joko Widodo ya dauki shari’ar da matukar muhimmanci.
Asirin malamin ya tonu ne bayan iyayen wata daliba sun kai karar sa wurin ’yan sanda cewa ya yi wa ’yarsu fyade har ta dauki juna biyu a shekarar da ta gabata.
A lokacin bincike ne aka gano ya yi wa kananan yara da dama fyade a makarantar, yawancinsu ’ya’yan talakawa masu kimanin shekara biyar a duniya.
Lauyoyin gwamnati sun bukaci a yi wa Herry Wirawan dandaka tare da yanke masa hukuncin kisa, amma ya nemi kotu ta sassauta masa domin ya samu damar kula da ’ya’yansa.
A kawo Wirawan kotun ne a daure da ankwa a yayin da Mai Shari’a Yohannes Purnomo Suryo Adi ya yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.
Kotun ta kuma umarci gwamnatin kasar da ta biya diyya ga iyalan yaran da aka yi wa fyaden.
Hukumar Kare Kananan Yara ta Indonesiya ta ce hukuncin da kotun ta yanke ya yi adalci ga yaran da aka cin zarafinsu.