Hankali ya tashi a garin Kubwa da ke Abuja kan cin zarafin wani malamin makarantar Islamiyya tare da tsare shi a ofishin ’yan sanda na tsawon sa’o’i kan ladabtar da dalibarsa ta hanyar yi mata bulala.
Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadin makon jiya, kamar yadda Aminiya ta samu labari, ya biyo bayan bulalar da malamin ya yi wa dalibar mai shekara 12 a lokacin da suke karatu, kamar yadda wani daga cikin malaman makarantar, ya bayyana.
- Shafin Trust Plus: Gayyata ta musamman ga masu bibiyarmu
- Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a Damboa
“Malamin ya yi nufin yi mata bulala ce a baya, amma sai ta tare bulalar, ta same ta a hannu.
“Bayan wani lokaci sai yarinyar ta koma gida, kuma ba a jima ba sai mahaifinta ya je makarantar ya tunkari malamin da magana.
“Washegari, ranar Litinin ne yayyenta uku wadanda tsofaffin daliban makarantar ne suka zo suna nemansa.
“Sun hango shi yana tafiya sai kawai suka yi kansa da motar da suke ciki, kamar za su buge shi kafin suka yi birki a kusa da shi.
“Yana waiwayawa sai suka hau shi da duka,” inji shi.
Wani da ya ga lamarin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce daga bisani malamin mai suna Sanusi ya kai maganar ga babban ofishin ’yan sanda na garin Kubwa tare da wani abokin koyarwarsa a makarantar, inda aka nemi su koma ofishin a washegari Litinin.
“Da suka koma sai kawai ’yan sanda suka tsare malamin tare da wanda ya yi masa rakiya bisa zargin karya wa yarinyar hannu, a sanadin bulalar da ya yi mata,” inji shi.
Aminiya ta samu labarin cewa, sai dai bayan an dauki hoton hannun yarinyar da na’urar asibiti kamar yadda bangaren malamin suka bukata, an gano cewa babu karaya a hannunta sai dai kumburi.
Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan Kubwa, CSP Bello Abdullahi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya shafi bangarori biyu ne, inda kowane ya shigar da kara.
Sai dai ya ce dukkan bangarorin biyu sun janye maganar daga bisani, sannan aka saki malamin tare da abokinsa.
Ya ce su ma matasan uku an tsare su kan dukan da suka yi wa malamin, kafin a sake su bayan yin sasanci.
Wadansu da Aminiya ta zanta da su, sun ce ofishin ya so mika malamin zuwa hedikwatar ’yan sanda ta Abuja da nufin kai shi kotu, sakamakon tsayawar iyayen yarinyar tare da ikirarin an karya mata hannu.
“Amma sai suka sauya shawara saboda tsayawar wadansu malamai da shugabanni bayan hoton kashi da aka yi mata ya nuna cewa babu karaya a hannun,” inji majiyar.
Wani jagora a Kungiyar Makarantun Islamiyya ta Kubwa da aka zanta da shi, ya ce ba a kai ga yanke shawarar ko za a karbi dalibar ko akasin haka a tsakanin sauran makarantun Islamiyya da ke yankin ba.
Gabanin aukuwar lamarin dai, dalibar tana karatu ne a makarantar ce tare da wadansu ’yan uwanta hudu maza da mata.