Wata jinjira ‘yar wata uku na kwance a asibiti sakamakon fyade da aka yi mata bayan an sace ta daga hannun mahaifiyarta a kauyen Adogi da ke jihar Nasarawa.
“An tsince a wani kango da dan kamfanta a gefe, ko’ina a gabanta jini na fitowa, daga nan muka garzaya da ita asibiti”, inji mahaifiyar yaririyar.
Yanzu an yi wa jaririyar aikin tiyata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), sakamakon mummunan raunin da ta samu.
Mahaifiyar jaririyar da aka yi wa fyade ta ce abun ya faru ne da tsakar dare bayan sun yi barci sun bar kofa a bude saboda tsananin zafi.
- Ya kamata a dandake masu yin fyade — Minista
- An yi fyade 299 cikin wata 5 a Adamawa — Likita
- Gwamnoni za su yi dokar ta-baci kan matsalar fyade
“Na farka da misalin 3.00 na dare na ga an dauke jinjirata…, na yi ihu, mutanen gidanmu da makwabta suka shigo suna mana jaje”.
Ta ce daga nan mutane a kafa da kan babura suka bazu neman diyar tata, wadda aka tsinta an jefar a wani kango.
Ta yi kira ga mahukunta da jami’an tsaro a jihar Nasarawa da su taimaka a kamo a kuma hukunta wadanda suka lalata mata diya.
Mahaifiyar ta ce bayan abin da aka yi wa diyar tata a ranar 27 ga watan Mayu, nan take suka sanar da ‘yan sandan Adogi amma har yanzu ba su tuntubi iyalan ba.
Amma Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce ba su da labarin abin da ya faru.
“Na kira ofishin ‘yan sanda da ke kula da Adogi amma suka ce ba a kawo musu rahoto ba, amma suna kara bincikawa”, inji shi.