Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), ta ce ta yi wa yara 191,222 aka haifa a jihar Gombe rajistar haihuwa a shekara guda.
Kwamishina a hukumar, Alhaji Abubakar Muhammad, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a jihar, yayin taron wayar da kai kan muhimmacin yi wa jama’a rajista, da kididdiga (CRVS).
- Kamfanonin hakar ma’adinai na China na kwace mana filaye – ’Yan Kamaru
- Sabon Shugaban Kenya ya soke biyan tallafin man fetur a kasar
Hukumar dai ta saba gudanar da taron ne duk shekara domin nuna muhimmacin wayar da kai kan rajista da kididdiga ga gwamnati da a tsakanin al’umma
A cewarsa, adadin da hukumar ta tara na baran kaso 76 ne na 2022.
Don haka ya bukaci al’umma da su gabatar da ’ya’yansu da ba su kai shekaru 17 da haihuwa ba ga hukumar domin rajistar sunayensu a hukumance kyauta, wadanda suka kai 18 zuwa sama kuma kan Naira 2,000.
A cewarsa, rajistar za ta ba da shaidar haihuwa zuwa mutuwa ne a dokance, da kuma tabbatar da samar da muhimman hakkokin bil-Adama ga jama’a.
“Wadannan hakkokin sun hada da na damawa da dan kasa da tattalin arziki hadi da hakkin samun damar ayyukan gwamnati,” inji Kwamishinan.
Ya kuma jaddada kudurin NPC na hada gwiwa da bangarori da dama domin wayar da kan mutane kan muhimmacin amfani da tsarin na CRVS.