✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Buhari ca kan rashin halartar jana’izar Janar Attahiru

Rashin ganin fuskar Shugaba Buhari a wurin jana’izar ya tayar da kura.

A ranar Asabar da ta gabata ne aka yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Maraigayi Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da da sauran manyan hafsoshi da dakarun soji 10 a Abuja, babban birnin kasar.

An yi jana’izar mamatan ne da suka rasu sakamakon hatsarin jirgin sama da ya ritsa da su ranar Juma’a a Jihar Kaduna.

Mutum shida aka yi wa Sallah a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja daga cikin 11 da hatsarin jirgin ya yi ajalinsu.

An kuma yi wa ragowar Kiristoci biyar tasu jana’izar a Babban Cocin Kasa da ke birnin na Abuja.

Manyan jami’an gwamna ne suka halarci jana’izar ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan, Babban Sufeton ’Yan sanda; Muhammadu Adamu, Ministan Sadarwa; Isa Pantami, Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe; Mai Mala Buni da sauransu.

Sai dai rashin ganin fuskar Shugaba Muhammadu Buhari a wurin jana’izar ya tayar da kura a dandalan sada zumunta musamman na Twiiter, inda ’yan Najeriya da dama ke bayyana ra’ayoyinsu gami da sukar Shugaban.

Wani mai amfani da sunan ChemAnthony @VoiceOfFrancee ya wallafa a shafinsa cewa, “Shugabanku na iya kai ziyara ketare saboda kowane irin dalili amma ba zai iya halartar jana’izar babban jami’insa ba wanda shi da kansa ya nada.

“Me ya sa Buhari yake yaudarar ’yan Najeriya kamar yana jin kunyarsu? ’Yan uwa akwai wani abun da ba a so mu sani.”

Wata Nefertiti @firstladyship, bayan ta wallafa hoton Shugaba Vladmir Putin na Rasha na halartar wata jana’izar dakarun soji yayin da ruwan sama na mamako ke sauka, ta ce, “Ga Putin nan yana halartar jana’izar sojoji ya jike sharkaf.

“Amma Buhari bai iya halartar jana’izar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya ba, alal akalli ko don ya kara wa dakarun soji kwarin gwiwa.

“Tabbas Bayo (mai daukar hotunan Shugaba Buhari) ya yi bakin cikin rashin samun irin wannan dama da zai dauki Bubu (Buhari) irin wancan hoto mai kyau, irin wannan asara har ina.”

Shi kuwa Hadimi na musamman ga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri cewa ya yi, “Abin takaici ne a ce Janar Buhari bai halarci jana’izar Janar Attahiru ba, sai dai Ministan Tsaro ne ya wakilce shi.

“Attahiru ya mutu yana yi wa kasar nan hidima, Buhari ya je Paris (Faransa) ya yi kwanaki hudu, amma ba zai iya halartar jana’izar Attahiru wacce ba za ta dauke shi sama da minti 30 ba.”

Wani kuma Muhammad El-Bonga Ibrahim @el_bonga ya wallafa cewa, “Idan har Buhari zai tafi har zuwa Kasar Faransa, daya daga cikin wuraren da annobar Coronavirus ta fi tsanani a Turai, to kuwa bay a da hujjar da za ta hana shi halartar jana’izar Marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, saboda haka fakewa da yana yi wa matakan kariya na cutar Coronavirus ladabi ba hujja bace.”

Uduak Iniodo @uiniodu ya wallafa cewa, “Na yi tsammanin Shugaba Buhari zai yi jawabi ga wa ’yan kasar a matsayin girmamawa ga Marigayi Babban Hafsan Sojin da sauran manyan sojoji da suka rasu suna bauta wa kasar nan, amma sai ga shi ko halartar jana’izar bai yi ba duk da kasancewarsa Babban Kwamandan Tsaro na Kasa.”

A wallafar da Comrade Deji Adeyanju @adeyanjudeji ya yi, ya ce “Duk wasu dabi’u da halayya na Buhari sun suna cewa ba ya son gwamnatinsa ta yi nasara, saboda haka yi masa addu’a da fatan samun nasara bata lokaci ne.”