✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe Babban Injiniyan ‘Federal Poly Bauchi’ a gidansa

Sun harbe shi a wuya, nan take ya ce ga garinku nan.

’Yan bindiga sun kashe Babban Injiniyan Kwalejin Fasaha da Kere-kere ta Tarayya da ke Bauchi, Abubakar Garba Muhammad, a gidansa.

Maharan sun kutsa gidan Injiniya Abubakar da ke unguwar Burshin Fulani, a kan hanyar Bauchi zuwa Dass, ne da daren Asabar, suka bude masa wuta.

A halin yanzu wani makwabcin mamacin da shi ma ’yan bindigar suka kai wa farmaki yana can kwance ana jinyar sa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH) da ke Bauchi.

Sanarwar rasuwar da hukumar gudanarwar kwalejin ta fitar ta ce,“Innalillahi Wainnailaihi Rajiun, ’yan bindiga sun kashe daya daga cikin ma’aikatanmu wanda shi ne Babban Injiniya, Abubakar Garba Muhammad (Babangida Birshi) da ke sashen tsare-tsare da misalin 2.30 na dare a gidansa da ke Burshin Fulani.”

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya ce mamacin ya rasu ne nan take bayan ’yan bindigar sun harbe shi a wuya.

Ya kara da cewa, “Jami’anmu sun je sun dauke shi suka garzaya da shi zuwa asibiti, amma ko da suka isa sai likita ya tabbatar musu cewa rai ya riga ya yi halinsa.

A cewarsa, jami’ansu sun bazama domin kamo bata-garin da suka yi danyen aikin don su girbi abin da suka shuka.

Harin dai ya haifar da zaman dar-dar a tsakanin mazauna unguwar ta Burshin Fulani.

Wani mazaunin unguwar, Ibrahim Mohammed, ya ce, “Wannan harin ya haifar da tsoro sosai a Burshin Fulani saboda mu dai ba mu taba ganin irin wannan kazamin abu ba. Saboda haka muke roko ga hukuma da ta tsaurara matakan tsaro a yankin.”