✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi ‘taron makon farko’ don yara da mata masu ciki a Neja

Burin kowace gwamnati a kowane mataki musamman a wannan kasar shi ne, ta samar wa jama’ar da ke karkashinta shirin ingantaccen kiwon lafiya, domin a…

Burin kowace gwamnati a kowane mataki musamman a wannan kasar shi ne, ta samar wa jama’ar da ke karkashinta shirin ingantaccen kiwon lafiya, domin a samu irin al’ummar da za a yi alfahari da ita, wadda za ta kasance cikin walwala.
Yara kanana da mata su ne a sahun baya wurin samun kulawar da ta kamata a wannan fannin mai matukar muhimmanci, muddin aka yi la’akari da yaran da ba su haura shekara biyar ba da kuma mata masu dauke da juna biyu.
Ganin irin wadannan wahalhalun da suke fama da su ne, Gwamnatin Tarayya a shekarar 2010 ta ware mako guda don gudanar da makon yara a Asaba babbar birnin Jihar Delta. Daga nan aka ci gaba da ware mako guda duk bayan wata shida domin kula da lafiyar yara da mata masu ciki.
Abubuwan da ake ba su sun hada  da magungunan tsutsar ciki da sinadarin bitamin A da kuma auna lafiyar mata masu juna biyu. Ana rarraba musu gidan sauro da yi wa jarirai rajista, tare da ba su shawarwarin irin abincin da za su rika ci da yadda za su kula da lafiyarsu.
A makon da ya gabata ne Jihar Neja ta bi sahun sauran takwarorinta wurin kaddamar da shirin kashi na farko da aka yi a asibitin garin Maikunkele hedikwatar karamar Hukumar Bosso inda iyaye suka yi tururuwa  domin kawo ‘ya’yansu a duba lafiyarsu daga ranar 16 zuwa 20 ga wannan watan.
Har ila yau a wurin kaddamar da shirin ne, aka kaddamar da shirin yi wa yaran da ba su haura shekaru 5 da haihuwa ba allurar riga-kafin shan-inna da jami’an kiwon lafiya suka bi gida-gida domin gudanar da aikinsu daga ranar 21 zuwa 24 na wannan watan.
Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, wanda ya samu Wakilcin Kwamishiniyar Ma’aikatar Kula da Lafiya Hajiya Hadiza Abdullahi ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su bayar da ‘ya’yansu, domin su ci moriyar wadannan shirye-shirye kiwon lafiyar biyu, wadanda ya nuna hanya ce da idan aka bi ta za a samu nasarar kai wa ga daya daga cikin muradun karni na rage yawan mata da ke mutuwa yayin da suka zo haihuwa da kuma yara kanana.
Gwamnan ya yaba wa Shugabannin addini da na al’umma ganin yadda suka tashi tsaye suka wayar da kan jama’a, suke ci gaba da amincewa da manufofin gwamnatin da aka yi musu tanadi.
Ya bayyana takaicinsa ganin yadda wasu iyaye ke amfani da addini wajen hana a yi wa ’ya’yansu allurar riga-kafin cutar shan-inna, wanda ya tuna wa taron cewa kasashen Najeriya da Pakistan da na Afghanistan su ne kasashen da suke fama da cutar shan-inna.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Kula da Lafiya Hajiya Hadiza Abdullahi wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Dokta Mahmud Ndatsu Muhammad ya karanta sakonta, ta shaida wa jama’a irin hadarin da ke tattare laulayin rashin lafiya a-kai-a-kai da kuma amfanin nau’o’in abinci masu gina jikin da za su ci da ’ya’yansu ba tare da sun kashe kudi mai yawa ba.
Ta bayyana takaicin ganin yadda mata masu yawa suke kin amfani da gidan sauron da aka rarraba musu. Ta ce wannan yana daya daga cikin manyan dalilan suka sa ake ci gaba da samun matsalar cutar zazzabin cizon sauro.
Ta ce ya zama wajibi su kara azama tare da sa wa jami’an kiwon lafiya ido, domin su rika yi wa jama’a bayanan muhimmancin da ke tattare da amfani da gidan sauro.
Wasu daga cikin iyaye mata wadanda suka kai ’ya’yansu domin  a ba su magungunan da suka dace da su a makon farko da kuma allurar riga-kafin shan inna a mako na biyu, sun tabbatar da cewar suna samun amfani da yawa daga irin wadannan shirye-shiryen.