✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi taron addu’o’i kan matsalar tsaro da tattalin arziki a Jigawa

Ɗaruruwan mutanen da suka halarci addu’ar ta musamman sun nuna damuwarsu kan makomar Nijeriya.

Wata ƙungiya da aka fi sani da Sawaba Humanitarian Initiative ta gudanar da taron addu’o’i na musamman domin kawo ƙarshen rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki da suka jefa ‘yan Najeriya cikin halin ni-’ya-su.

An gudanar da addu’ar ne a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa a yayin da duk ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na daƙile masu shirya taron ya ci tura.

Ɗaruruwan mutanen da suka halarci taron sun nuna damuwarsu kan makomar ƙasar ganin yadda talauci, yunwa da cututtuka ke kashe mutane a kullum yayin da masu riƙe da madafun iko ko kuma masu mulki ba su nuna damuwa a kai ba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban Ƙungiyar Sawaba Humanitarian Initiative na Ƙasa, Kwamared Umar Danjani Hadejia ya ce al’amura a ƙasar nan na ƙara taɓarɓarewa ga talaka.

“Na kasa shawo kan hawayena bayan ganin yunwa na yi wa tsofaffi da mata da yara a ƙauyukan Jihar Jigawa illa.

“Babu wani shugaban siyasa mai tunani da zai yi barci cikin kwanciyar hankali bayan ya ga abin da na gani a ƙauyuka da dama,” in ji shi.

Danjani ya ce ya damu matuƙa da irin wahalhalun da ya gani a waɗansu unguwanni, inda magidanta ke jinginar da kadarorinsu don cin abinci, yayin da wasu kuma ke kwashe kadarorin domin dawainiyar gidajensu.

Yadda aka gudanar da salloli da addu’o’in a birnin Dutse.