Wani rikici mai nasaba da addini ya barke tsakanin wani mutum da makotansa a Unguwar Dorayi Babba da ke Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.
Ana zargin lamarin wanda ya faru a yammacin Litinin ya samo asali ne sakamakon adawar da mutanen unguwa ke yi wa mutumin wanda mabiyin Shi’a ne kan wani fili da ya mallaka a unguwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, wasu mazauna unguwar ne ke adawa da taron da mabiya Shi’a kan gudanar a filin nasa kuma suka nemi a daina, lamarin da ya jawo har aka kona motar mutumin.
“Bayan ya ki daina gudanar da tarukansa sai mutane suka nemi sayen filin kan baira miliyan 12 amma sai ya ki aminta.
“Suka sake cewa sun saya naira miliyan 15 nan ma ya ce ba zai sayar ba.
“Mutamin ya ce zai sayar amma kan naira miliyan 50, daga bisani kuma ya ci gaba da gudanar da tarukansa sai kuma kwatsam ya fusata ya kona motarsa da kansa,” a cewar wasu mazauna unguwar.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ’Yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni an cafke mutum hudu da ake zargin sun haddasa tashin fitinar.
Ya ce bayan samun rahoton abin da ke faruwa nan take aka aike da jami’an ‘yan sanda wajen domin kwantar da tarzoma.
“Bayan samun kiran neman agajin gaggawa, Kwamishinan ‘yan sanda CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya aike da jami’anmu karkashin jagorancin Shugaban ‘yan sandan unguwar Dorayi Babba.
“Da isar su wurin suka samu nasarar kwantar da tarzomar sai dai sun samu an kone motar mutum kirar Toyota Corolla,“ a cewar DSP Kiyawa.
Ya kara da cewa wasu mutane da suka ji rauni an garzaya da su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed inda aka ba su kulawa sannan daga bisani aka sallame su.