Daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar marigayi Usman Ahmad Hassan da ake zargin ’yan ina da kisa sun yi wa kisan gilla a kusa da rukunin gidajen Larix da ke unguwar Karmo a Abuja.
Margayin ma’aikacin Sashen Albarkatun Man Fetur (DPR) ne, kuma an kashe shi ne da safiyar Lahadi a lokacin da yake tattaki.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 bayan karbar kudin fansa a Taraba
- San da aka turke don Kirsimeti ya yi kisa a Bayelsa
Aminiya ta gano cewa an tsinci gawar matashin ne a kusa da unguwar da yake zaune da iyalinsa.
Da yake bayyana kaduwarsa da rashin, mahaifin margayin, Hussaini Ahmad, ya ce, “Matar ce ta kira ni ranar Lahadi cewa ba a ga Usman ba tun safe da ya fita.
“Daga baya aka kira ni wai an tsinci gawarsa, daga nan aka kawo ta Barikin Ladi mahaifar margayin da ke Jos muka yi masa sallah.”
Shugaban Matasan Barikin Ladi, Danjuma Ibrahim, ya ce, “Mun kadu da samun labarin rasuwar, musamman kuma yanayin kisan da ya kasance abin tausayi ne saboda an yi shi ne ba tare da nuna imani ba.
“Mutumin kirki ne ba ga danginsa kadai ba, har ma da kowa da kowa, shi ya sa ma dubban mutane suka zo jana’izarsa