✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar tsohon Shugaban Karamar Hukumar Lere, Ramin Kura

Alhaji Ramin Kura ya rasu ya bar mata 3 da ’ya’ya 38.

An yi jana’izar tsohon Shugaban Karamar Hukumar Lere, Alhaji Aliyu Saleh Ramin Kura da ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin.

Dubban mutane da suka hada da ‘yan siyasa da manyan sarakuna da manyan ’yan kasuwa da malaman addini daga wurare daban daban ne suka halarci jana’izar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a ranar Talata a garin Ramin Kura.

Alhaji Ramin Kura, ya rasu ne a yammacin ranar Litinin, a wani Asibiti da ke Abuja bayan doguwar jinya.

Marigayin wanda ya bar Duniya yana da shekaru 68, ya rasu ya bar mata 3 da ‘ya’ya 38.

Marigayin ya rike mukamin Shugaban Karamar Hukumar Lere har sau biyu, kuma ya rike mukamin Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA).

Haka kuma ya rike mukamin mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna Ahmed Muhammed Makarfi shawara na musamman.