✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar Sarkin Tangale Na 15

An yi bison gawar Mai Tangle Dokta Abdu Buba Mai Sheru II da ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata 10 ga watan Janairu,…

An yi bison gawar Mai Tangle Dokta Abdu Buba Mai Sheru II da ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata 10 ga watan Janairu, 2021 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Mai Tangle Dokta Abdu Buba Mai Sheru II wanda aka yi bisonsa cikin jimami a Makabartar Kirista da ke garin Billiri a ranar Asabar 16 ga Janairu, 2021, shi ne Sarkin Tangale na 15 da ya zama Sarki na tsawon shekara 19 kafin rasuwar sa makon jiya.

Tsohon gwamnan jihar Gombe ne Abubakar Habu Hashidu ya nada shi Sarautar Mai Tangle kuma ya bashi sanda a lokacin da aka nada shi mai Tangle na 15.

Takaitaccen tarihin Mai Tangale na 15

An haifi Mai Tangle ne a unguwar Poshiya da ke Karamar Hukumar Billiri a Jihar Gombe.

A nan ya yi karatunsa na Firamare a tsakanin shekarar 1962 zuwa 1968 bayan ya gama sai ya tafi garin Ibadan inda ya halarci cibiyar koyon rubutu da keken rubutu wato typist a 1970 zuwa 1971, ya samu shaidar Grade II.

Bayan nan ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna a shekarar 1974 ya gama a shekarar 1977 ya samu takardar shaidar babbar Difloma a bangaren Girke-girke.

Kafin mutuwarsa, ya yi aikace-aikace da damatun a rusasshiyar jihar arewa a shekarar 1971 zuwa 1974.

Ya kuma zama jami’i na musamman a bangaren girke-girke a gandun Daji na Yankari da ke Bauchi a shekarar 1975 zuwa 1976.

Ya kuma rike mukaddashin manajan otal din Wild Life Hotel Board a Bauchi sannan daga baya ya samu aiki da Kamfanin Siminti na Ashaka a 1979 inda ya yi ta samun karin girma har ya kai manaja a Kaduna da Bauchi da Yola da Zariya.

Kana daga bisani aka kara masa girma aka mayar da shi hedikwatar kamfanin a 1990 zuwa 1992.

Marigayi mai Tangle ya zama jami’i mai kula da zirga-zirgan motocin kamfanin siminti na Ashaka na farko a shekarar 1994 zuwa 2001 inda ranar 24 ga watan Mayu 2001 aka nemi ya zama sarki ya gaji kakansa ya zama Mai Tangle na 15.

Dokta Abdu Buba Mai Sheru II ya mutu ya bar matar aure daya Misis Festa Abdu Buba Mai Sheru da ’ya’ya 6.