✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar Kakar tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama

A ranar Talata, 30 ga watan Maris, aka gudanar da jana’izar Sarah Obama, kishiyar kakar tsohon shugaban Amurka, Barack Obama. Sarah wacce ta raini mahaifin…

A ranar Talata, 30 ga watan Maris, aka gudanar da jana’izar Sarah Obama, kishiyar kakar tsohon shugaban Amurka, Barack Obama.

Sarah wacce ta raini mahaifin tsohon shugaban tamkar dan cikinta, an sanya ta a gidanta na karshe da tsakar ranar Talata a bisa koyarwar addinin Islama.

Kamfanin Dillancin Labarai na EPA ya ruwaito cewa, a cikin daren ranar Lahadin da ta gabata ne Sarah ta riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekara 99 a duniya.

’Yarta mai suna Marsat, ta ce ta rasu ne a Asibitin Jaramogi Oginga Odinga da ke yankin Kisumu a Kasar Kenya.

Tsohon shugaban na Amurka ya bayyana kaduwarsa da mutuwar kakar tasa wacce ake kira da Mama Sarah.

Yayin da ake sanya Marigayiya Sarah a makwanci
Yayin da ake yi wa gawar Marigayiya Sarah addu’a

“Ni da iyalin muna jimamin rasuwar kakarmu abar kaunarmu, Sarah Ogwel Oyango Obama, wacce aka fi sani da ‘Mama Sarah’ amma mu mun fi kiranta da ‘Dani’ ko ‘Kaka’.”

“Za mu yi matukar kewarta,” a cewar Obama cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Marigayiyar ta sha kare Obama a lokacin zaben Amurka yayin da aka rika zargin cewa shi Musulmi ne kuma ba a Amurka aka haife shi ba.

Ta kuma yi fafutikar ganin an inganta ilimin ’ya’ya mata da marayu a kauyenta na Kogelo.