✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar Adamu Fika a Kaduna

An birne shi ne a Unguwar Sarki da ke Kaduna

An yi jana’izar marigayi tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Wazirin Fika, Malam Adamu Fika a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne ya jagoranci sallar janaza da yammacin Laraba.

Mal Adamu Fika ya rasu ne a daren Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya yana da shekaru 90 da duniya.

Daruruwn mutane ne suka samu halartar sallar jana’izar da aka yi masa da misalin karfi 4:15 na yamma, cikinsu har da mai bai wa shugaban Kasa Shawara a fannin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, wanda shi ne ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya.

Kazalika, daga cikin tawagar akwai Ambasada Babagana Kingebe da Kuma shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Jalal Arabi da sauransu.

Sannan akwai manyan jami’an gwamnati daga Yobe da kuma hakimai da suka samu halartar sallar janazar.

Sheikh Gumi ya bayyana marigayin a matsayin abin koyi, inda ya ce samun irinsa cikin shugabannin yanzu abu ne mai wahala.

Dan haka ya yi masa addu’ar samun Aljannar Firdausi .

Shi ma Nuhu Ribadu ya bayyana rashin marigayin a matsayin babban rashi ga kasa wanda hakan ya sa Shukagan Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aiko su domin jajantawa iyalansa da kuma kasa baki daya.

An birne marigayi Adamu Fika ne a makabartar Unguwar Sarki inda kuma mutane da yawa suka samu halartar.