A ranar Litinin da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa (FA) ta Ingila ta fitar da jadawalin gasar cin Kofin Kalubale ta Kasar.
Jadawalin ya nuna za a yi wasanni zagaye na uku ne a ranakun 4 da 5 ga watan Janairu mai zuwa.
Kuma ya nuna mai rike da kofin wato Manchester City za ta kece raini ne da kulob din Port Bale da ke wasa a rukunin ’yan dagaji yayin da Chelsea za ta shawo ta da kulob din Nottingham Forest. Kulob din Liberpool kuma zai hadu ne da na Eberton yayin da Arsenal zai shawo ta da Leeds United. Manchester United kuma za ta hadu ne da kulob din Wolbes wadda ta doke United a matakin kwata-fainal a gasar a bara.