✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi holen masu laifi 331 a Kano

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi holen wasu mutum 331 da ta kama kan zargin aikata miyagun laifuka a cikin wata daya. Kwamishinan ’yan…

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi holen wasu mutum 331 da ta kama kan zargin aikata miyagun laifuka a cikin wata daya.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Abubakar Lawal Daura ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Bompai a birnin Dabo.

CP Daura ya ce sun ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su, da mutane 11 da aka yi yunkurin fataucinsu, da kuma kayayyakin da aka sace wanda suka hada da motoci, wayoyi, babur mai kafa 3, da kuma muggan makamai.

Ya ce rundunar ta yi nasarar kama mutanen ne a sakamakon hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da muggan laifuka a jihar.

A cewarsa, ababen zargin da rundunar ta kama sun hada da masu garkuwa da mutane 69, ’yan damfara 12, masu fashi da makami 5, masu fataucin mutane 7, barayin mota da babur 18, sai kuma ’yan daba guda 168.

Wadansu ababen zargi da suka shiga hannu
Wasu daga cikin ababen zargin da aka cafke
Wani wanda ake zargi da laifi da kuma wasu kayayyakin da aka kwato a hannun ababen zargi
Bindigogi da aka kwato a hannun ababen zargin
Wasu miyagun makamai da aka kwato a hannun ababen zargin

 

“Daga cikin abubuwan da mukayi nasarar kwatowa daga hannun wadannan masu aikata muggan laifuka akwai bindigogi 27, sai kuma motoci 24, babur mai kafa uku guda 12 da kuma muggan kwayoyi da sauran makamai,” inji Kwamishinan.

Ya kara da cewa, rundunar za ta ci gaba da iya bakin kokarinta don ganin an yaki miyagun laifuka a jihar.

Kazalika, ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ci gaba da ba su gudummawa domin kawar da ayyukan bata gari.