✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da yara 3 da kashe 2 a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake yin garkuwa da yara uku da kashe mutum biyu a kauyen Yebu…

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake yin garkuwa da yara uku da kashe mutum biyu a kauyen Yebu da ke karamar Hukumar Kwali  cikin babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin unguwar mai suna Ayuba Danlami, ya ce  abin ya faru ne da tsakar daren yau Talata da misalin karfe 1:33 lokacin da ‘yan bindigar dauke da muggan makamai suka shiga unguwar.

Ayuba, ya ce  ‘yan bindigar sun kai hari wani gida a unguwar inda suka kashe mutum biyu sannan suka yi awan gaba da yara uku duk ‘yan gidan.

An kashe mutanen lokacin da suke kokarin fita daga cikin gidan don neman agajin makwabta, nan ta ke ‘yan bindigar suka bude masu wuta.