’Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado.
Maharan sun yi awon gaba da Farfesa Onje Gye-Wado ne da misalin karfe 12 kafin wayewar garin ranar Jum’a a gidansa da ke unguwar Gwagi a Kamarar Hukumar Wamba ta jihar.
Wani daga cikin iyalan tsohon mataimakin gwamnan ya ce maharan sun fasa katangar gidan ne suka shiga ta dakin matarsa suka tafi da shi.
A baya Farfesa Onje Gye-Wado wanda ya kasance mataimakin gwamann Jihar Nasarawa daga 1999 zuwa 2003 ya sha tallake tarkon masu neman yin garkuwa da shi.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce runduarsu ta tashi haikan da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin ceto tsohon mataimakin gwamnan cikin koshin lafiya.
Ya roki jama’a da ke da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen ceto tsohon mataimakin gwamnan da ya sanar da jami’an tsaro.