✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Shugaban Miyetti Allah na kasa

’Yan bindiga sun je har gidanshi suka tafi da shi da bakin bindiga.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah na Kasa, Alhaji Wakili Damina. 

Sakataren Kungiyar, Adamu Abubakar ya sanarwa a ranar Talata cewa an wasu ’yan bindiga sanye da kakin sojoji sun yi awon gaba da Damina ranar 30 ga watan Afrilun 2021.

Wasu da abun ya faru kan idonsu sun ce, ’yan bindigar su kusan takwas a cikin wata motar bus ne “suka yi amfani da karfin tuwo” suka fito da Damina daga gidansa da ke kauyen Chikara da ke Jihar Kogi da misalin karfe 12 na rana.

Abubakar ya ce wani kanin Damina da abin ya faru a kan idonsa ne ya sanar da shi kimanin awa daya bayan masu garkuwar sun yi awon gaba da shi.

Abubakar ya ce, nan take ya gwada kiran wayar ta shugaban na Miyetti Allah amma ba ta shiga.

“Tun daga wannan lokacin wayarsa ba ta shiga kuma mun yi ta kokarin gano inda yake amma abun ya gagara,” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa sun sanar da Kwamishinan ’Yan Sanda da Gwamnatin Jihar ta hannun me ba gwamna shawara kan harkokin tsaro, Jerry Omodara.

Da aka tuntubi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ede Ayuba, don jin ta bakinsa sai ya ce har yanzu jami’ansu ba su kai ga gano inda Damina yake ba.

Ayuba ya bayyana cewa, sun yi kokarin neman karin haske ta bakin shugaba me kula da ofishin ’yan sanda na yankin da abun faru, amma ya ce ba su da masaniyar faruwar lamarin a hukumance.