Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Edo, sun yi sace shugaban ma’aikatan jihar, Mista Anthony Okungbowa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a birnin Benin, babban birnin jihar yana tsaka da tafiya da akan motar sa.
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila a jihar Edo
- An cafke masu garkuwa da mutane a Edo
- An ware kwanaki 7 don farautar ‘yan ta’adda a Edo
- An sace Shugaban Karamar Hukuma da wasu mutum 13 a Edo
Maharan dai sai da suka harbe direban sa kafin su yi garkuwar da shi.
Wata majiya daga cikin jami’an tsaro ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce bincike ya nuna ayyukan ‘yan bindiga ne.
Sai dai majiyar ta ce kawo yanzu ba a kai ga samun cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru ba.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ta Edo, Mista Babatunde Kokumo da kuma Kakakin Rundunar, amma ya ci tura samu saboda kin daukar wayar.
A watan Mayun 2020 ne dai Gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya nada Okungbowa a matsayin shugaban ma’aikatan jihar.