✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da shugaban karamar hukuma a Nasarawa

An yi garkuwa da shugaban karamar hukumar ne tare da wasu da dama a hanyar Andaha zuwa Akwanga a ranar Litinin.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa, Safiyanu Andaha.

Aminiya gano cewa an yi garkuwa da shugaban karamar hukumar ne tare da wasu da dama a hanyar Andaha zuwa Akwanga a ranar Litinin.

Cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wani fitaccen attajiri, Adamu Umar, wanda aka fi sani da Maccido.

Majiyar ta ce ’yan bindigar sun bullo daga cikin cikin daji ne suka, tare su suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Kawo yanzu dai ba su tuntubi iyalai ko makusantan wadanda aka sacen ba.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa, Rahman Mandela, amma hakan bai samu ba.