✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da shugaban Fulani a Kwara

An yi awon gaba da shugaban Fulanin yayin ziyarar 'yan uwansa.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Fulani, Alhaji Usmanu Sule, wanda aka fi sani da Jamhuro Lamba a Lalate a Karamar Hukumar Ibarapa ta Jihar Oyo.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an sace mutumin mai shekara 90 ne a duniya lokacin da ya kai wa ‘yan uwansa ziyara a kauye.

  1. Matashi ya kone kansa saboda ya gaza biyan kudin jarrabawa
  2. ’Yan bindiga sun harbe Shugaban kasar Haiti Jovenel Moise

“‘Yan bindigar sun shigo kauyen amma shi kadai suka dauka duk da cewa a lokacin yana tare da mata da kananan yara.”

Abubakar Malam Boggol, wani mazaunin garin Lamba a jihar Kwara, ya shaida wa Aminiya cewa Jamhuro Usmanu Sule shi ne shugaban duk wani Jamhuro da ke jihar Kwara.

Ya ce lakabin ‘Jamhuro’ ana bawa shugaban Fulani da ya dade zaune a kasar Yarabawa.

Ko da wakilinmu ya tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Oseifo Adewale, game da lamarin ya ce yana wajen wani taro saboda haka ba zai iya magana ba sai daga baya.