✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da Sakataren Hukumar Zabe a Nasarawa

'Yan bindigar sun shiga har cikin gida yayin garkuwa da shi.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da sace Sakataren Hukumar Zaben Jihar (NASIEC), Mohammed Abubakar Opu.

Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Rahman Nansel ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Lafiya, babban birnin Jihar.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an kai wa rundunar ‘yan sandan jihar rahoton sace sakataren da misalin karfe 1 na ranar 25 ga Agustan 2021.

“An shigar da rahotn cewar wasu ‘yan bindiga su biyar sun shiga gidan sakataren  da ke kauyen Bakin Rijiya sannan suka yi garkuwa da shi.

“Tuni kwamishinan ‘yan sanda ya tura kwararrun jami’an ‘yan sanda zuwa yankin don gudanar da bincike,” a cewar sanarwar.

Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro sun bazama wajen domin ceto shi daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.