Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani bawan Allah da matarsa a yankin Ukya Sabo da ke Karamar Hukumar Toto, a Jihar Nasarawa.
Wani mazaunin yankin mai suna Samuel ya shaida wa Aminiya, cewa ‘yan bindigar sun dauke mutanen ne da misalin karfe 1 na daren Asabar.
- Abduljabbar da malaman Kano: An tashi ba a cimma matsaya ba
- Yadda barayi suka addabi majinyata a asibitin Gombe
Ya ce ‘yan bindigar sun yi wa yankin kawanya, daga bisani suka haura katangar gidan mutumin sannan suka yi awon gaba da sho da matarsa.
“Sun haura gidan mutumin sannan suka shiga har cikin dakinsa, inda suka yi awon gaba da shi da matarsa,” a cewarsa.
Ya ce yayin ficewa daga yankin, ‘yan bindigar sun yi ta harbin iska ta yadda suka razana makotan mutumin, daga bisani kuma suka yi daji da wadanda suka sace.
‘Yan sanda ba su da masaniya
Aminiya ta gano wanda aka sace din, mai suna Yohana Isheme, ma’aikaci ne a Sashen Lafiya na Karamar Hukumar Toto, yayin da matarsa kuma malamar makarantar firamare ce a yankin Tika.
Shugaban Sashen Yada Labarai na Karamar Hukumar Toto, Mista Gabriel Hagai, ya tabbatar wa da wakilinmu sace magidancin shi da matarsa ta wayar tarho.
Sai dai kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya ce ba shi da masaniya game da lamarin.