✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da matar basarake a Kano

’Yan bindiga sun shiga kauyen Tsara da ke Karamar Hukumar Rogo a Masarautar Karaye, tare da yin garkuwa da matar Mai Garin, Aisha Aliyu. Hakimin…

’Yan bindiga sun shiga kauyen Tsara da ke Karamar Hukumar Rogo a Masarautar Karaye, tare da yin garkuwa da matar Mai Garin, Aisha Aliyu.

Hakimin Rogo, Dagacin Karaye Alhaji Muhammadu Mahraz ne ya bayyana wa Sarkin Karayem, Alhaji Ibrahim Abubakar II faruwar lamarin.

Masarautar Karaye ta fitar da jawabi dauke dasa hannun Jami’in Yada Labaranta, Haruna Gunduwawa, cewa ’yan bindigar sun dauki tsawon lokaci suna harbi a iska, kafin su yi awon gaba da matar mai garin.

Sakon ya ce maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 1 na daren Talata, lamarin da ya tilasta wa mazauna kauyen tserewa su buya a cikin daji har zuwa wayewar gari.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Aminiya cewa, ba su labarin lamarin, amma da zarar labarin ya iske su za su sanar.