Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wata matar aure da kanwarta a unguwar Sabon Gero da ke Sabon birnin Kaduna.
Lamarin wanda ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Litinin wannan ya jefa akasarin mazauna unguwar cikin tashin hankali.
Aminiya ta fahimci cewa, mijin matar baya gidan a lokacin da maharar suka dira gidan nasa saboda yana aiki ne a Abuja.
Wakilinmu da ke a yankin ya shaida mana cewa, maharar sun fice daga unguwar da bayan sun fahimci jama’a sun ankara kuma sun fara taruwa domin tin kararsu.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da uwa da danta a Abuja
- An yi garkuwa da hakimi da mutum biyu a Plateau
- An yi garkuwa da mutum 7 lokacin da ake maraba da Gwamnan Taraba
“Mijin matar baya gida a lokacin da suka shiga da kanwarsa suka dauka suka fice daga gidan tun kafin jama’a su cinmasu.
“Ko da na kira wasu a unguwar cikin daren sun tabbatar min da cewa matar da kanwar mijinta aka dauka, ” in ji shi.
Ya kuma bayyanawa Aminiya cewa, ko a ranar Litinin da ta gabata maharar sun shiga garin Doka inda suka sace Sarkin garin da wani mutum da diyarsa.
Dan haka sun nuna dai akwai bukatar gwamnatin jihar ta kawowa mazauna yankin sabuwar Kaduna watau Kaduna Millennium City da ke a karamar hukumar Chikun dauki.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’Yan Sandan jihar Mohammed Jalige ya ce zai nemi karin bayani wajen DPO na yankin kafin ya ce wani abu.