✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mataimakin shugaban APC na Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kaduna Alhaji Shuaibu Idris Lauje tare da ’yarsa Sadiya Shuaibu a gidansa da…

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kaduna Alhaji Shuaibu Idris Lauje tare da ’yarsa Sadiya Shuaibu a gidansa da ke Kwanan Zango a karamar hukumar Igabi a Jihar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na daren ranar Alhamis.

Rahotanni sun shaida cewa sai da ’yan bindigan suka yi harbe-harben kan mai uwa da wabi kafin su shiga gidansa suka fito da shi da ’yarsa.

A yanzu haka dai babu wanda ya san inda aka kai mataimakin shugaban da ’yarsa domin ’yan bindigan ba su tuntubi iyalinsa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce suna binciken yadda za a karbo mahaifin da ’yarsa.