’Yan sanda a Jihar Neja sun tabbatar da yin garkuwa da masunta 13 da wasu ’yan bindiga suka yi a kauyen Kwanar Barau da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.
Kwanar Barau dai na kan hanyar Tegina zuwa Minna a Jihar ta Neja.
- Najeriya a Yau: Wane tsarin zabe ya fi dacewa a Najeriya?
- BUK za ta fara yin takin zamani da iskar gas daga dagwalon masana’antun fata
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Monday Kuryas ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna.
Ya ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 3:30 na yamma, lokacin da baturen ’yan sandan yankin ya ba da rahoton cewa wani direban wata mota kirar bas ne ya kai rahoton lamarin.
A cewar Kwamishinan, motar mai cin mutum 18 mai lambar LGT12XWX ta dauko fasinjojin ne, wadanda yawancinsu masunta ne, daga Yawuri a Jihar Kebbi.
Masuntan dai na kan hanyarsu ta zuwa Jihar Bayelsa ne domin kamun kifi, lokacin da lamarin ya ritsa da su a kauyen.
Kuryas ya ce direban ya shaida musu cewa a wata kwana mai matukar hatsari suka ci karo da masu garkuwar, sanye da kayan sojoji, inda suka yi awon gaba da fasinjojin, ciki har da yaron motarsa.
Kazalika, masu garkuwar sun kwace wa direban kudinsa da yawansu ya kai N131,500.
Sai dai Kwamishinan ya ce tuni jami’ansu suka shiga farautar masu garkuwar, inda ya bukaci mutane, musamman mazauna yankunan karkara da su tallafa musu da bayanan da za su kai ga kamo su. (NAN).