Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani mutum mai suna Hamidan Habu a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan a Dutse a safiyar Laraba.
“Ranar 6 ga Yuni da misalin karfe 1:30 na dare, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Hamidan Habu mai shekara 55, a kauyen Shengel da ke Ringim zuwa wani wuri da ba a sani ba.
“Sai da suka yi harbe-harbe a iska kafin su tafi da shi daga kauyen da ke da nisan kilomita 25 da garin Ringim,” a cewar Shisu.
Daga baya jami’an ’yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka gano fankon harsashi.
A cewar kakakin, ’yan sandan na ci gaba da bincike tare da bin sahun wadanda suka yi awon ga a da mutumin don cafke su.