✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Mai Daukar Hoton Gidan Gwamnatin Ebonyi

Masu garkuwa da shi suna neman kudin fansa Naira miliyan 50

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Mai Daukar Hoton Gidan Gwamnatin Jihar Ebonyi, Mista Uchenna Nwube, a kan hanyar Okigwe-Aba zuwa Enugu.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauke mai daukar hoton ne da misalin karfe 7 na dare ranar Laraba.

’Yan bindigar sun ba shi damar yin magana da iyalansa ta wayar tarho inda ya shaida musu cewa, “An yi garkuwa da ni da wasu mutane lokacin da nake komawa Abakaliki daga Aba.

“Sun ce suna bukatar kudin fansa Naira miliyan 50, wanda ni ban san yadda zan yi na samu wadannan makudan kudade ba; Ina rokokn a taimaka min.”

Sai dai kakakin ’yan sandan Jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna kokarin sun ceto mutumin da sauran wadanda aka yi garkuwa da su din.

“Yankin da lamarin ya faru ba ya karkashin ikonmu, yana karkashin kulawar jihohin Imo da Abiya ne, amma duk da haka muna yin iya bakin kokarinmu,” cewar Anyanwu.