✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mahaifin shugaban karamar hukuma a Abuja

'Yan bindigar sun shiga yankin da misalin karfe 1 na dare, sannan suka yi awon gaba da tsohon.

Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun shiga yankin Tokolo dake Karamar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tararra Abuja, inda suka yi garkuwa da mahaifin shugaban Karamar Hukumar, John Gabaya.

Wata majiya daga cikin iyalan shugaban ta shaidawa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Talata.

A cewar majiyar, “Baba, wanda tsohon malamin makaranta ne, ba wanda ya taba tsammanin haka zata faru da shi.

“Bayan sun yi garkuwa da shi, ana zaton a kafa suka tafi da shi saboda babu wanda ya hangi abun hawa da suka zo da shi,” in ji majiyar.

Ya kara da cewa ’yan bindigar da adadinsu zai kai 15 sun yi wa yankin kawanya tare da tare duk wata hanyar fita daga cikinsa.

Daga nan ne bayan daukan lokaci suna harbe-harbe a iska, wasu daga cikinsu suka shiga gidan tsohon mai shekaru 85, sannan suka yi awon gaba da shi.

Baturen ’Yan Sanda na yankin Bwari, CSP Biodon Makanjuola, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce suna kokarin ganin sun ceto tsohon daga hannun ’yan bindigar.