✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da iyalan dogarin Atiku

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ce ’yan bindiga sun yi garkuwa da mata da kuma dan jami’inta da ke tsaron tsohon Mataimakin Shugaban Kasa,…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ce ’yan bindiga sun yi garkuwa da mata da kuma dan jami’inta da ke tsaron tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Shaidu sun ce maharan sun kutsa gidan Sajan Hammandikko Nyako da ke unguwar Yolde Pate a garin Yola, suka yi awon gaba da iyalansa a ranar Litinin da dare.

Majiyar ta ce da maharan ba su ga jami’in wanda suke zaton yana gida ba, sai suka yi awon gaba da matarsa da dansa da bakin bindiga.

Wan Sajan Hammandikko kuma Shugaban Masu Rinjaya a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Hammantukur Yetisuri shi ma an yi garkuwa da shi a gidansa da ke unguwar Jada Mbulo.

Da misalin karfe biyu na daren Laraba ne ’yan bindigar da ke neman kudin fansa Naira milya 50 suka yi wa gidan Hammantukur kawanya suka tafi da shi.

Kakakin ’Yan Sanda na Jihar, Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce rundunar yaki satar mutane da ta Operation Farauta na bin sawun miyagun don kubutar da mutanen biyu.