’Yan ta’adda sun yi garkuwa da Honorabul Kabiru Onyene, sanannen hadimi ga tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Hon. Kabiru a ofishinsa da ke garin Okene da misalin karfe 7 na dare, bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Wani ganau ya ce “kwatsam muka jin harbe-harbe, jama’a sun fara guje-guje, shi ne muka gane cewa karar bindiga ne.
“Bayan ’yan mintoci sai muka ji harbe-harben a wurin ofishin Kabiru, inda suka tafi da shi.
- Arewa ba za ta raga wa Tinubu a 2027 ba —Atiku
- Yadda dillalai ke zagon ƙasa ga shirin tallafin kayan noma
“Amma abin mamaki shi ne wurin da abin ya faru kusa yake da wani shingen binciken sojoji a kusa da gidan tsohon gwamna,” in ji shi.
A safiyar Talata wani dan kabilarsa ya wallafa a kafar sada zumunta cewa, “A taya mu da addu’a, jiya da dare an yi garkuwa da dan uwana Honorabul Kabiru Onyene, daga ofishinsa.
“Allah (SWT) Ya kare shi Ya kuma yi wa hukumomi jagoranci su kubutar da shi da wuri domin ya dawo cikin iyalansa.”
Iyalan dan siyasan sun ce masu garkuwar ba su tuntube su ba, lamarin da ya kawo fargaba.
Mun tuntubi kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, game da lamarin amma ya ce ba shi da labari, sai dai ya bincika.
Sai dai kuma har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari ba mu ji daga gare shi ba.