✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da direban ofishin Mataimakin Gwamnan Nasarawa

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani direba da ke aiki a Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani direba, Daniel Ogoshi, wanda ke aiki a Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa.

An yi garkuwa da Mista Daniel Ogoshi ne a kafin wayewar garin Laraba a gidan wani abokinsa da ke Karamar Hukumar Lafia ta Gabas ta jihar.

Aminiya ta gano cewa maharan sun bar motarsa da wayarsa a wurin da suka dauke shi.

Wani mai kusanci da ’yan uwan direban ya ce dan uwan Ogoshi ne ya sanar da shi abin da ke faruwa inda suka sanar da ’yan sanda, amma kafin su isa wurin ’yan bindigar sun riga sun yi awon gaba da shi.

Kakakin mataimakin gwamnan jihar, Christopher Ehima, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce ya girgiza su kuma gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin kubutar da Ogoshi.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce rundunar ta fara farautar ’yan bindigar domin ceto direaban.

A kwanan ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Onje-Gye Wado, wanda suka sako bayan an biya kudin fansa Naira miliyan hudu.