’Yan bindiga sun yi garkuwa da dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Kuros Riba a Jam’iyyar YPP, Yarima Agbor Onyi, a jajibirin zaben gwamna.
An yi awon gaba da da shi ne a yammacin ranar Alhamis a kan hanyar Akparavuni, wadda ta yi kaurin suna wajan ayyukan masu farkuwa da mutane a Karamar Hukumar Biase.
- Yadda sojoji suka gudanar da Musabakar Al-Kur’ani a Borno
- Ashe amaryar da ake cewa ta yi kankanta bazawara ce?
Sakataren YPP a jihar, Fredrick Omari, Rahotanni sun bayyana cewa garkuwa da dan takarar suna ta kwan gaba, kwan baya kan batun kudin fansa.
Ya nuna kaduwa game da garkuwa da dan takarar a jajibirin zabe, yana mai kira ga jami’an tsaro su dauki matakin da ya dace wajen wajen kubutar da shi cikin gaggawa.
Hakan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun sako Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar, Farfesa Gertrude Njar da ta shafe wata daya a hannun masu garkuwa da ita, bayan an biya kudin fansa.